<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Hatton, John (1710-1793), Watts, Isaac (1674-1748)</author>
<hymn_number>242</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Dukan sarautar duniyan nan,
 Da ikonta da girmanta,
 Game da kai, Mai Cetona,
 Ba na maishe su kome fa.

[V2]
 2) Ƴanuwana da abokaina
 Ba su da hanyar taimako,
 Amma a bisa giciye
 Yesu ya gama fansata.

[V3]
 3) I, jinin Yesu ne kaɗai
 Wanda ya shafe laifina,
 Mai yawan ƙauna hakanan,
 Ba waninsa a duniyan nan.

[V4]
 4) Haƙuri, ƙauna, taimako,
 Koyarwa, iko, gafara,
 Zuciya mai tuba, ceto duk,
 Shi Yesu ne mai bayarwa.

[V5]
 5) Ya Yesu Ubangijina,
 Nan gaba bawanka na ke.
 Zuciyata, raina, ƙaunata,
 Na ba ka duka, naka ne.</lyrics>
<title>Dukan Sarautar Duniyan Nan LW242</title>
</song>